2023: Ba ni da asara don APC ta ruguje – Badaru Abubakar

Karatun minti 1
Badaru Abubakar
FILE: Badaru Abubakar - Gwamnan Jigawa (APC)

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa rikice-rikicen jami’iyyar APC a jihar Jigawa ka iya kawo rugujewar jami’iyyar a shekarar 2023.

Gwamnan ya ce idan jami’iyyar ta ruguje sakamakon rikicin cikin gida ba shi da asara a kai domin a cewarsa shi dan kasuwa ne.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake rantsar da shugabannin riko na jami’iyyar a matakin kananun hukumomi a ranar Juma’a.

Ya kara da cewa hakurinsa ya kare bisa rarrabuwan kai da ake samu a cikin ‘ya’yan jami’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin cikin gida ne ya kai ga cire tsohon shugaban jami’iyyar, Habibu Sara a wani taro da masu ruwa da tsakin jami’iyyar suka gudanar a fadar gwamntin jihar a watan Satumbar da ta gabata.

An zargi tsohon shugaban da nuna goyon baya ga tsagin Sanatan Jigawa ta Arewa, Sabo Nakudu.

Gwamna Badaru ya ce; “Zan cigaba da lura da yadda wasu daga cikinku suke shiga tattaunawa da wancen tsagin, hakuri na ya kare, kuma ba zan sake lamuntar hakan ba.”

“Ni dan kasuwa ne, zan iya tafiya duk inda nake so a duniyar ba tare da na dauki jaka ba, sai dai idan na so.”

Kazalika gwamnan ya yi kira ga daya tsagin jami’iyyar da su dawo su cigaba da hada hannu da karfe wajen ciyar da jami’iyyar gaba.

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog