0
Mai ɗakin shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta ƙaddamar da nata goyon bayan akan zanga zangar dake gudana yanzu haka a fadin Najeriya mai taken #Achechijamaa wato “A Chechi Jama’a”.
Dabo FM ta rawaito hakan na zuwa ne bayan Aisha Buhari ta sanya wani bidiyo da yake nuna shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a ciki tare da sauran shuwagabannin tsaro a shafukan ta.
Bidiyon dai na ɗauke da wata waƙa dake bayyana abubuwan dake faruwa a Arewacin Najeriya, “Dan Allah a duba, Arewa na kuka, ana zubar da jinin mu.”
Zuwa yanzu dai kusan jihohon Najeriya suna cigaba da zanga zangar lumana domin kawo ƙarshen matsalolin da suka ddabi ƙasar.
