/

Fityanul Islam ta taya Sabon Sarkin Zazzau murna

dakikun karantawa

Hadakar kungiyoyin darikun sufaye karkashin jagorancin kungiyar fityanul Islam ta kasa raeshen Jihar Kaduna da kwamitin shirya zagayen mauludi na garin Zariya da kwamitin shirya Tafsirin Al-qur’an mai girma na kofar fadar Sarkin Zazzau da Kuma iyalan gidan Marigayi Sheikh Abdulkadir Zariya sun kai ziyarar taya murna ga sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a fadar sa da ke cikin birnin Zariya.
Ziyarar da ta gudana bisa jagorancin wakilai daga matakin kasa da jiha da kuma karamar hukuma ta kungiyar.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitowa ziyarar taya murnar da kuma mubayi’ar, Shugaban kungiyar fityanul Islam ta kasa reshen Jihar Kaduna Malam Rabi’u Abdullahi Zariya, ya ce lokacin rasuwar Marigayi Mai Martaba Sarki Alhaji Shehu Idris sun zo ziyarar ta’aziyya da nuna alhini na rashin Uba ga Kasa baki daya, kuma suka yi addu’an Allah rahimin Sarki ya gafarta masa ya sa yana kyakkyawan matsayi.
Shiyasa kuma da aka sanar da magajin shi, suka sake zuwa domin taya murna da jaddada goyon bayan da suke baiwa Sarakuna iyayen kasa ga sabon Sarkin domin kaiwa ga manufofin da ake bukata na ciyar da addinin musulunci gaba.

Kuma suka bayyana yanayin kyakkyawan danganta da mu’amala da suka yi da Marigayi Sarki musamman lokutan gudanar da tarukan su a baya, suka kuma yi fatan sabon Sarkin zai daura a kan inda Marigayi ya tsaya.

Malam Rabi’u Zariya ya kuma yi addu’an samun dawwamammen zaman lafiya a lardin Zazzau da Jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya.

Sa’ilin ziyarar Sheikh Sani Khalifa Zariya shi ma ya tunatar da sabon Sarkin muhinmancin hadin kai da yin duk mai yiwuwa wurin sanya addu’o’i gaba saboda samu zaman lafiya mai daurewa a masarautar Zazzau, Kuma ya yi addu’a ta musamman ga Sabon Sarkin Ambasa Ahmad Nuhu Bamalli da ‘yan majalisar sa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog