Masu shirya fitaccen shirinnan na Labarina sun sanar da fara ɗaukar cigaban shirin kashi na 3.
Babban mai bayar da umarni a shirin, Aminu Saira ne ya sanar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.
Darktan ya ce nan ba da daɗewa ba, za zu sanar da masoyan shirin lokacin da zai riƙa zuwa garesu.
Ya ce; “Cikin yardar Ubangiji, mun fara ɗaukar shirin LABARINA mai dogon zango kashi na 3.
“In sha Allah ba da jimawa ba, za mu sanar da ku lokacin da za a dawo haska muku shi. Ku taya mu da addu’a.
Shi ma Nazifi Asnanic, daya daga cikin masu ɗauƙar nauyin shirin, ya nemi al’umma su taya su addu’a a kan shirin.
Labarina, shiri ne da ya samu karɓuwa wajen masoya fina-finan Hausa musamman gabannin fara sarara dokokin kullen Korona a Najeriya.
Masana na ganin shirin ya shiga jerin shaharareun fina-finan shekarar 2020.
