Home LabaraiInyamurai ba makiyanmu bane, lokaci ya yi da za mu hada kai – Kwankwaso

Inyamurai ba makiyanmu bane, lokaci ya yi da za mu hada kai – Kwankwaso

by Dabo Online
0 comments

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa yankin kudu maso gabashin Najeriya ba makiyan ‘yan arewa bane. Ya kuma buƙaci ƴan Najeria su manta da abubuwan da yaƙin basasar Najeriya ya haifar a dukkanin bangarorin Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana cewar yankunan guda biyu su na da ɗaɗaɗɗn tarihin siyasa a tsakaninsu, in da ya ce yanzu lokaci ya yi da ya kamata a farfaɗo da wannan tsohuwar alaƙa mai tsawon shekaru.

Tsohon gwamnan Kanon ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da sashen Igbo na BBC wadda aka wallafa a ranar Laraba. Ya ce, sassauci, yafiya, da kuma tafiya su ne su ka wanzar da zaman lafiya a tsakanin shugabannin bayan an ƙare yaƙin basasar Najeriya.

Ya jaddada cewa Najeriyaba za ta taba ci gaba ba idan har za a bar ta ta kasance cikin fargaba da rashin amincewa da juna wajen yin kabilanci tsakananin shiyyoyi. Ya ƙara da cewa shugabannin Arewa na baya sun dade da fahimtar muhimmancin yin aiki tare da yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Kwankwaso ya ce, “Dole ne mu yafe wa junanamu. Dole ne mu yi aiki tare a matsayin yan uwa. Yankin Kudu maso Gabas sun daɗe su na zama abokan ƙawancenmu kuma aminai na shekaru da dama.

Tsohon Ministan Tsaron ya kawo misali da jamhuriya ta farko, inda ya nuna cewa jam’iyyar Northern People’s Congress (NPC), wadda ta fi alaƙantuwa da Arewa, ta kulla kawancen siyasa da jam’iyyar National Council of Nigerian Citizens (NCNC) karkashin jagorancin shugaban kasar Najeriya na farko, Nnamdi Azikiwe.

A cewarsa, wannan hadin gwiwa ya nuna cewa shugabannin siyasa na wancan lokacin sun sanya haɗin kan kasa gaba da maslahar ƙabilanci.

Kwankwaso ya kuma tuna cewa bayan kawo karshen mulkin soja a karshen shekarun 1970, shugabannin siyasa sun rungumi sulhu ta hanyar sanya ‘yan Kudu maso Gabas a cikin shugabancin ƙasa duk da raɗaɗin da yaƙin basasa ya bari. Ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN), ciki har da tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari, sun yi aiki tare da ‘yan siyasar Kudu maso Gabas har ta kai ga marawa marigayi Dr. Alex Ekwueme baya ya zama Mataimakin Shugaban Kasa.

“An gama yakin basasa a shekarar 1970. Lokacin da tsarin dimokuradiyya ya dawo a 1978 da 1979, abu na farko da shugabanninmu su ka ce shi ne, ‘Waɗannan fa ba makiyanmu ba ne. Bari mu nuna musu hakan ta hanyar dawo da su mu yi aiki tare.’ Haka shugabanninmu na jamhuriya ta farko su ka yi aiki tare da su har suka kawo Alex Ekwueme ya zama mataimakin shugaban kasa,” in ji shi.

Da yake magana kan alakarshi ta ƙashin kai da Ekwueme, Kwankwaso ya bayyana marigayin a matsayin aminin Arewa na kusa, yana mai tunawa da yadda ya halarci jana’izarsa a garin Oko da ke Jihar Anambra.

Haka kuma, Kwankwaso ya kawo misali da dawowar tsohon shugaban Biafra, Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, daga gudun hijira a matsayin wata alama ta sulhu bayan yaki, inda ya bayyana cewa shugabannin Arewa sun tarbe shi har ma aka ba shi damar shiga cikin harkokin siyasa inda ya tsaya takarar Sanata duk da cewa bai yi nasara ba.

A karshe, Kwankwaso ya yi kira da a guji siyasar addini, kabilanci ko shiyya-shiyya, inda ya bayyana cewa babu wani bangare guda daya da zai iya mulkar Najeriya shi kadai.

“Ba za mu iya kasancewa a kasa daya muna fada ba. Dole ne mu kasance da ran yafiya ga duk wanda ya yi wa wani ba daidai ba,” in ji shi, yana mai jaddada cewa Arewa tana farin cikin komawa ga tarihi don yin aiki tare da Kudancin Gabas, ba tare da hakan ke nufin suna fada da Kudancin Yamma ko wani bangare na kasar nan ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00