0
A cigaba da tattara sakamakon zaben wuraren da aka sake zabe a jihar Kano, INEC ta dage zaman zuwa 8 na safiyar Lahadi, 24/03/19.
Baturen zaben ya bayyana hakan ne bayan cimma matsaya da wakilan jami’iyyu bisa rashin kawo wasu kananan hukumomi.
Hukumar ta tsayar da tattara sakamakon da karfe 1 na daren Asabar.
Ana dai dakon isowar sakamakon mazabar GAMA ne dake karamar hukumar Nassarawa.
