Home LabaraiA gaggauce: Akwai yiwuwar bayar da sanarwar ajiye azumi a Najeriya

A gaggauce: Akwai yiwuwar bayar da sanarwar ajiye azumi a Najeriya

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Biyo bayan sanarwa da Sarkin Musulmi, Abubakar Saad II ya fitar na tabbatar da daukar azumi yau Asabar, akwai yiwuwar sake duba lamarin ganin wata.

Kwamitin da yake lura da ganin wata a Najeriya, National Moon Sighting Committee ya fitar da sanarwa neman wadanda suka ga wata a jiya Juma’a a fadin Najeriya.

Kwamitin da ya fitar da sanarwa a shafin Facebook yace dukkanin wanda ya san ya ga wata a fadin tarayyar Najeriya to ya sanar kwamitin domin tattara bayanai domin mikawa mai alfarma Sarkin Musulmi.

“Idan kana daga cikin wanda ya gajinjirin wata jiya Juma’a a fadin Najeriya, ko kuma ka san wanda ya tabbatar da ganin wata ko wasu mutane, tare da sanin yadda za a samu ayi magana da su, to ya tuntube mu.”

“Membobin kwamitin ganin wata zasu tuntubesu domin su tattaunawa domin suyi aikinsu wajen bayar da shawara ga mai alfarma Sarkin Musulmi domin sauke hakki.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00