Labarai

Kwabid19: Bazan yafewa wadanda suka bata min suna ba -Amb. Kabir Rabi’u Dansitta

Mutumin da aka zarga da shigo da Koronabairos jihar Kano, Ambasada Kabiru Rabi’u Dansitta ya bayyana cewa ba dai dai bane a ce shine ya kawo cutar jihar ba.

Kamar yadda majiyar Dabo FM cikin wata tattaunawa da Ambasadan yayi da DailyTrust, ya bayyana akwai yiyuwar a jihar Kano ya samu cutar dalili kuwa shine ya shafe kwanaki 12 a jihar kafin a gwada shi aga yana dauke da cutar.

“Gaskiya bana ji zan yafewa wanda suka bata min suna, abin ya bani mamaki yanda wasu mutane suka dinga fadin wai saida aka harbeni a wajen killace mutane a lokacin da nake kokarin guduwa, kuma nazo kano ne domin neman maganin raunukan da alburushi yayi min.”

“Ciki harda mutanen dake fadin wai saida na je wurare don tabbatar da na yadawa al’umma wannan cuta, bazan iya yafewa wadannan mutane da suka bata min suna ba.”

Ya kuma kara da cewa baima kamata a bayyanawa duniya sunansa ba, wanda ya zargi manyan ma’aikatan gwamnatin jihar da bayyanawa duniya sunansa..

Karin Labarai

UA-131299779-2