Sarkin Musulmi Saad III
Ra'ayoyi

Ko dai a dawowa da Sultan alfarmarsa, ko ya zare hannunsa a komai, Daga Hassan Ringim

Lokacin da Shehu Dan fodio ya kaddamar da jihadi, duk kasashen da ya mamaye(‘yanto), to ya kan bawa wanda zai jagorancesu(Amir) alkur’ani mai girma da kuma takobi. Wannan yanayi aka ci gaba da bi, har lokacin khalifofinsa. Kai tsaye, daga daular Sokoto ake bayar da umarnin amincewa da nadin Sarki ko tsigeshi daga kan mulki.

To amma bayan kamar shekaru dari haka, da turawa suka tarwatsa wancan tsari, sai aka bawa gwamna damar nada Sarki ko tsigeshi. Wannan yanayi ne, ya kawomu a yau muke ta fama da matsaloli marasa dadi dangane da addininmu da kuma al’adarmu.

A wancan lokaci, Sultan(Sarkin Muslmai) shi yake bayar da sako ko umarnin gabatar da wasu ayyukan ibada(kamar daukar azumi da saukewa da sauransu). Sai dai da turawan Ingila suka yi mana ta’adi, sai suka bar Sultan da fadin ganin wata da saukewa. Nada Sarki da cireshi ya koma hannun bature. Hakan na nufin samun iko cikakke don biyan bukatunsu.

A yau abin da muka wayi gari kenan. Ga dai Sultan can a garkame a Sokoto, amma ba shi da ikon komai akan sarakunan Musulmai, kamar yanda Dan fodio ya assaso. Haka Sultan yake ganin ana yi wa sarakunan Musulmai cin fuska da wulakanci, amma ba damar magana. Ko da yake shi ma din bai wuce a yi wasa da alfarmarsa ba(kamar yanda muka gani a zamanin Abacha).

Idan har kuwa an wayi gari a haka, to ya kamata a sake duba makomar alfarmar Sultan. Sanar da ganin watan Ramadan da Shawwal duk shekara bai dace da yanayin da muke ciki a yanzu ba. Idan da hali, tun da har gwamnonin kasa ne suke da ikon nadin Sarki, to ya kamata a ce shugaban gwamnonin Najeriya ya zama shine zai na fadin ganin wata don daukar azumi da saukewa.

Abin takaici shine, a jiya (Juma’a) an ga wata a sassa da dama na Arewa har da su kasar Zazzau, amma wai sai Sarki Shehu Idris yace shi ba shi da ikon fadin wata ya kama, sai dai Sultan.

Amma idan ta hadosu da gwamnati, yanzu El-rufa’i sai ya cireshi. Kuma Sultan yana can Sokoto rike da carbi
Abin ma takaicin shine, yanda Saudiya ta samu damar mamayemu a bulus, domin ta fahimci wannan gibi da kuma rauni da Sultan ya samu. Sai ta yi amfani da kungiya ta shigo Najeriya, ta ke yin rawar gaban hantsinta yanda ta ga dama!

DABO FM ba ta da hurumi, goyon baya ko rashinsa akan abinda marubucin ya rubuta.

Karin Labarai

Masu Alaka

‘Yan siyasa na amfani da kalmar “Hassada” ko “Bakin ciki” don dakushe masu musu hamayya

Dabo Online

Romon Dimokradiyya: Kura da shan bugu Kato da kwace kudi, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

Anyi kira ga Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II da ya janye kalamanshi akan satar Yara a Kano

Dabo Online

Meyasa wasu mutane suke jin tsoron tofa albarkcin bakinsu wajen kawo gyara a siyasa?, Daga Umar Aliyu Musa

Dabo Online

Ko faduwar Atiku zata zama tashin Kwankwaso?

Dangalan Muhammad Aliyu

Ba Kwankwaso ne basa so ba, cigaban Talaka ne yake musu ciwo – Dangalan Muhammad Aliyu

Dabo Online
UA-131299779-2