Jami’an tsaro a jihar Bauchi sun kama shugaban kungiyar daliban jihar Bauchi ‘NUBASS’ kuma tsohon dan takarar shugaban daliban jami’ar Bayero, Adamu Musa Kaloma a yau Asabar, DABO FM ta tabbatar.
Majiyoyi sun tabbatarwa da DABO FM cewar an kama matashin ne bisa gayyata domin jagorantar zanga-zangar lumana a kan gwamnatin jihar ta biya dalibai basussukan da daliban jihar suke binta na ‘Scholarship’ da kuma neman gwamnatin jihar ta sahale domin a koma makarantu a fadin jihar.
DABO FM ta tabbatar da cewa an shirya gudanar da zanga-zangar ne a ranar Litinin, 27 ga watan Yuli, 2020.
Kazalika shugaban daliban, Kaloma, ya yi ta shelantar zanga-zanga ta kafofin sada zumunta ciki har da ‘Whatsapp Status.’
Cikakken bayanin yana zuwa…..