A guji yada jita-jita: Sheikh Dahiru Bauchi bai zagi Buhari akan rufe iyakoki ba

Da safiyar yau Asabar, an wayi gari da wani labarin da wata tashar Youtube mai suna Gimbiya TV ta wallafa wani bidiyo inda ta sa masa sunan “Kabude Bodar tinda ba ta Uban*** bace, inji Dahiru Usman Bauchi.

An dai rika yada tsagwaron karyar a shafukan Facebook.

Sai dai abin lura anan shine, shafin ya sanya sunan ne tare da cewa kalaman malamin basuda alaka da sunan bidiyon da suka sanya.

DABO FM ta binciko cewa; an dauki bidiyon malamin ne a dai dai lokacin da yake yin addu’a tare da wasu manyan malamai da jami’an Gwamnatin Najeriya a kasar Saudiyya.

Ga dai ainahin abinda malamin yace; “Babban abinda yake kanku, ku masu damar ganin shugaban kasa Buhari, kuce masa ya bude kasa a rika shigo mana da abinci.”

A bangaren mutane, da dama saboda kiyyarsu ga Gwamnatin shugaba Buhari, suia rika turawa suna jin dadin bisa yacce babban malamin yayi magana akan rufe bodar.

Masu Alaƙa  In Sarki ya kira dan siyasa mutumin kirki, masu hamayya zasu ce yana goya masa baya - Dr Pantami

Wasu kuma a bangarensu, lamarin sai yayi musu dadi, domin suna ganin babu girma a jikin babba mai mutumci da yake zagi ba.

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.