Labarai

A matsayi na, na ‘dan Dagaci, tayaya mutane zasu ce zan rushe ko ruguza Masarauta? – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Umar Abdullahi Ganduje ya bada tabbacin cewa karin masarautu 4 da jihar tayi yana nan daram kuma babu abinda zai tarwatsa shi, kuma yayi sune a bisa niyya mai kyau.

Ya bayyana haka ne a Lahadi, inda yake bayani na cewa a yanzu Sarkin Kano,Muhammad Sunusi II, ba shine Sarki mafi daraja a Kano ba.

Ya bayyana jin dadinshi bisa nadin sababbin masarautu 4, ya kuma kalubalanci masu cewa yaci mutuncin masarautar jihar Kano.

“A matsayi na na ‘dan Dagaci, ta yaya zanyi abinda zai bata zuriyar mu daddiya mai dumbin tarihi?

“Idan kuka bi salsala ta, akwai a kalla Dagatai 10 har zuwa mahaifina. To shiyasa nakerasa gane kan mutanen da suke cewa gwamnati ta tana kokari ruguza gidan da yake mai tarihi.

DaboFM ta tattaro bayanai na cewa Gwamna Ganduje yayi wannan jawabi ne a yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai fadar Sarkin Rano bisa rasuwar uwargidar, mai shari’a Wada Rano, Hajiya Wada Rano, bayan ya kammala zuwa gidan dangi mai rasuwar.

Ganduje ya kara bayyana cewa anyi karin masarautun ne badan komai ba sai dan kaiwa wuraren cigaba na zamani.


Ya tabbatar da cewa; “Zamu zo da sabbin hanyoyin wajen cigaban jiharmu. Irin wanna hanyar da zata kusantar damu(Mutane) zuwa ga masarautun mu. Shiyasa mukaga dacewar kara samun wadannan masarautun.”

Daga karshe, gwamnan ya baiwa Sarkin umarnin hukunta Hakimin Bebeji da yayi bore na kinyin mubaya’a ga sarkin.

“Idan har ta tabbata ya ajiye, Sarki sai ya turo nada wakilinshi kafin a nada wani.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Manyan bukatu 5 da Ganduje yake so majalisa ta zartar masa kan masarautar Kano

Muhammad Isma’il Makama

Sarkin Kano, Muhammad Sunusi II ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki a Birtaniya

Dabo Online

Gwamnonin Arewa suna tattaunawa kan shawo tsakanin Ganduje da Sarki Sunusi -Shatima

Dabo Online

Masarautar Kano ta kira taron Addu’ar cika shekaru 5 da rasuwar Marigayi Ado Bayero

Dabo Online

Babbar Kotu a Kano ta ‘rugurguje’ karin Sarakuna 4 da Ganduje ya kirkira

Dabo Online

Sandar da Sabbin Sarakunan Kano suke rikewa “Kokara” ce – Kwankwaso

Dabo Online
UA-131299779-2