Sule Lamido ya caccaki Obasanjo akan sukar Musulunci da ‘Yan Fulani

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya mayarwa da Olusegun Obasanjo martanin maganar da yayi akan yin amfani da Boko Haram da sauran manyan lafuka wajen yunkurin yaduwar Fulani da musulunci.

Sule Lamido ya bayyana haka ne a wata sanarwa mai dauke da saka hannun mai magana da yawunshi.

DaboFM ta hada cewa; da farko Sule Lamido ya shawarci Obasanjo daya nesanci kanshi daga shiga rikicin addini ko wata kabila.

“Saboda rashin ji tuwarka da wannan gwamnatin karka dauka kafin kowa sanin duk abinda yake wakana a kasa.”

Lamido yayi wannan martani ne biyo bayan kalaman Obasanjo na cewa; ana amfani da kungiyar Boko Haram, sace-sacen mutane, safarar miyagun kwayoyi da makamai, wajen kokarin a yada kabilar Fulani da Musulunci ta karfi a nahiyar Afirika.

Obasanjo yayi wannan kalami ne a Cocin Synod dake Oleh, Isoko ta kudu a jihar Delta.

Sule Lamido ya kara da cewa;
“In da ba’a wajen taron addinin kayi maganar ba, to zamu iya dauka kuma mu hakura. Kada rashin jituwar da shugaban kasa yasa ka kayi tunanin zama wanda yafi kowa sani.

“Ka rike matsayinka na zama babba a kasa, matsalar rarrabuwar kanmu ta fara zama wani abin daban.

%d bloggers like this: