1
Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata mai wakiltar Yobe ta gabas, Ibrahim Gaidam, ya bayyana cewa dayawa daga cikin mayakan Boko Haram suna son ajiye makamansu.
Gaidam ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin wata ganawarshi da ‘yan jarida a birnin tarayya.
Sanatan ya kara da cewa dayawa daga cikin mayakan suna jin tsoron fitowa suce sun ajiye makamansu.
A makon da ya gabata, Sanata ya mika kudurin samar da cibiyar kula da tubabbun mayakan Boko Haram a Najeriya.
Yace; “Babu tantama, dayawa daga cikin ‘yan ta’addar sun tuba, dayawa kuma suna son tuba bisa damarmakin da aka samu. Kungiyoyin zaman kansu dayawa ne suka tabbatar da haka.”
