“Abacha, Ado Bayero, Buhari da Umaru Yar’adua, ba ‘yan Najeriya bane”

Gidan Rediyo Cool FM dake jihar Legas ya fitar da wani rahoto da cewa Gen Abacha, Marigari Mai Martaba Alhaji Ado Bayero, Shugaba Buhari da Umaru Yar’adua ba ‘yan Najeriya bane.

Gidan rediyo ya fitar da rahoto da yake dauke da tarihin wadanda sunayensu suka fito a rubutun, wanda yayi nuni da suna da alakar jini da wata kasa bayan kasar Najeriya.

Sunyi rubutun ne ta hanyar yin tambaya da amsa kamar yadda zaku gani a kasa;

Shin Sani Abacha dan Najeriya ne?
Amsa: A’a.
Abacha Shuwa Arab ne daga kasar Chadi, matarshi ta kasance ‘yar asalin kasar Yemen.

“Shin Marigayi Ado Bayero dan Najeriya ne?
Amsa: A’a
Kakanninshi sunyi hijira daga kasar Sierra Leone. Wadansu daga cikin ‘yan uwan marigayi Sarkin ‘yan Kamaru ne yau.

“Shin Marigayi Umar Musa Yar’adua dan Najeriya ne?
Amsa: A’a


Dangin Yar’adua sun samu sunansu daga Sarkin Katsina, lokacin da Sarki ya kirawo kakansu Umaru daga Maradin kasar Nijar. Cikin zolaya Sarki ya sakawa kakan Umaru sunan ‘Yar Adua, ma’ana “Dan Addu’a” a yaren Hausa.

Daga cikin dangin Yar’aua aka samu shuwagabannin Najeriya biyu, Umaru Musa Yar’adua da Shehu Musa Yar’dua.

Shima Shugaba Muhammadu sai yayi bayani domin akwai kyautuwar kasancewarshi dan kasar Niger.

Maganar zama dan Najeriya ko rashinshi a kwana kwanan nan ta samo asali ne tin bayan da jami’iyyar APC tace Alhaji Atiku Abubakar dan Kamaru ne.

Lamari da har yakai ga wata kungiya ta baiwa Atiku wa’adin kwana 21 domin ficewa daga Najeriya don komawa kasarshi ta kamaru.

%d bloggers like this: