//
Thursday, April 2

Abba K Yusuf yayi nasara a kotun Koli, bayan fatali da karar Ganduje akan gabatar da karin shaidu 8

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kotun Koli tayi fatali da karar Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje, akan hana PDP gabatar da karin shaidu 8 a gaban kotun sauraren zaben gwamnan jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin Alkalai 5 wanda Mai Shari’a Mary Odili, ta tabbatar da hukucin kotun daukaka kara na karbar shaidu daga karin mutane 8 da PDP da Abba Kabir Yusuf suka gabatar.

Tin dai a watan Yuli, jami’iyyar PDP da dan takararta Abba Kabir Yusuf suka garzaya kotu sakamakon rashin amincewar kotun sauraren korafin zaben gwamnan domin su kara yawan shaidu wanda zasu gabatar a gaban kotu.

Ranar 26 ga watan Yuli, kotun daukaka kara dake da zama a jihar Kaduna, ta baiwa PDP damar karin shaidun.

Masu Alaƙa  Kotu tayi cilli da bukatar PDP, ta tabbatar da El-Rufa'i a matsayin halastaccen gwamnan Kaduna

Tini dai dukkanin bangarorin PDP da APC, a ranar 18 ga watan Satumba suka kammala yiwa kotu dukkanin bayansu.

Itama a nata bangaren, shugabar kotun, Mai Shari’a Halima Shamaki ta bayyana da cewa kotu zata tabbatar da yanke hukunci a cikin kwanaki 180 da dokar kasa ta gayyadewa kotun sauraren korafin zaben gwamna.

A yayin tafka muhawara, lauyoyin jami’iyyar APC da na hukumar INEC, Ahmad Raji SAN, Alex Ezinyon da Ofiong Ofiong SAN, sun bukaci kotun da ta kori karar da PDP ta shigar bisa cewar PDP ta kasa bayar da hujjojin ikirarin da takeyi.

Sai dai a nashi bangaren, lauyan PDP, Kanu Agabi SAN, ya bayyana cewa karar da suka shigar mai sauki ce domin hukumar INEC ita kanta ta tabbatar da anyi zaben farko na 9 ga watan Maris lami lafiya.

Masu Alaƙa  ZabenKano: Kotu ta gayyaci Kwamishinan ‘Yan Sanda da hukumar INEC akan Shari’ar ‘Abba Gida-Gida’

Lauya Kanu ya kumayi nuni da cewa; hukumar INEC ta tabbatar da ta tattara sakamakon zabe tare da cewa dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf, shine wanda yake da rinjaye da yawan kuri’u a zaben farko.

Ya kara da cewa daga baya ne hukumar INEC ta soke akwatinan zabe 207 wanda hakan ya sabawa dokar zabe.

DABO FM ta tattaro cewa; Lauyan na PDP dai yace suna neman kotu ta tabbatar da dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020