Tarihi

Abubuwan da suka faru a Rana Irin ta Yau, 27 ga Satumba a fadin Duniya

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 1529 Sojojin Daular Usmaniyya suka isa kofar birnin Biyana inda Sarki Sultan Suleman, ya jagoranci farmakin farko da aka kai wa birnin. 

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 1590 aka zabi Urbanuna matsayin Paparoma na 7, inda ya rasu bayan kwana 13 ba tare da an yi bikin hawarsa kujerar shugabanci ba. 

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 1917 kwararren mai zanen hotuna dan kasar Faransa Edgar Degas, ya rasu a birnin Paris. 

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 1922 Sarkin Girka Konstantin Na 1 ya sauka daga karagar mulki bayan an ci galabar sa a wani yaki da ya yi da Turkawa a Yankin Anatoliya. Yorgos ne ya hau karagar mulki a matsayin dan gidan Sarki Konstantin. 

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 1961 sojoji suka yi juyin mulki a Siriya. Tuni dai sojojin suka bayyana cewa sun fita daga Hadaddiyar Jamhuriyar Larabawa wanda Masar da Jam’iyyar Siyasar Baas suka kafa. 

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 1971 aka yi bikin bude hanyar jirgin kasa tsakanin Turkiyya da Iran. Shugaban Kasar Turkiyya Cevdet Sunay da Sarkin Iran Pehlevi ne suka bude hanyar.

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 1998 aka fara anfani da Kanfanin Google.

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 2013 dan wasan kwaikwayon Turkiyya Tuncel Kurtiz, ya rasu.

Karin Labarai

Masu Alaka

Taskar Magabata: Tarihin mutuwar Sardauna shekaru 54 da suka gabata

Dabo Online

Galadiman Kano ya cika shekara biyar da rasuwa

Muhammad Isma’il Makama

Abubuwan da suka faru a Rana Irin ta Yau, 28 ga Satumba a fadin Duniya

Muhammad Isma’il Makama

Yau kwanaki 210 tin bayan zargin Kwamishinan Kano da warce takardar tattara sakamakon zabe

Dabo Online

Yau kwanaki 211 tin bayan zargin Kwamishinan Kano da warce takardar tattara sakamakon zabe

Dabo Online

Sheikh Jaafar, Aminu Kano, Dan Kabo, Rimi, Gwarzo – Fitattun da Kano ta rasa a watan Afirilu

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2