Abdulaziz Yari ‘ya gina rijiyar birtsatsai kan naira miliyan 325’

dakikun karantawa

BBC HAUSA

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya musanta bar wa sabuwar gwamnatin jihar da Bello Matawalle ke jagoranta bashin makudan kudade, da kuma bayar da wasu kwangiloli na boge.

Tsohon gwamnan ya ce “babu gaskiya ko kadan a cikin bayanan”, kuma an yi su ne domin a bata masa suna. 

Mai magana da yawunsa Malam Ibrahim Dosara ya shaida wa manema labarai a birnin Gusau cewa “zargin ba shi da tushe bare makama”. 

Kwamitin karbar mulki da Gwamna Bello Matawalle ya kafa ne ya bankado wasu bayanai da suka nuna gwamnatin Yari ta bar bashin ‘yan kwangila da ya kai naira biliyan 251.

Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin tsohon mataimakin Yari wanda ba sa shiri yanzu, Alhaji Ibrahim Wakkala, ya kuma ce daga cikin aringizon kwangilolin da aka yi har da gina rijiyoyin burtsatse a kan naira miliyan 325 ko wacce daya.

An dade ana ce-ce-ku-ce tsakanin kwamitin da kuma gwamnatin Yari tun bayan da jam’iyyar PDP ta dare karagar mulki sakamakon hukuncin Kotun Koli da ya soke dukkan zabukan fitar da gwani da APC ta yi a jihar, sannan ya umarni a bayyana wadanda suka yi na biyu a zabukan.

Abdulaziz Yari ya mulki jihar Zamfara tsawon shekara takwas daga shekarar 2011 zuwa 2019.

Ibrahim Dosara ya kara da cewa sun yi mamaki da kwamitin mika mulki bai shaida wa duniya cewa Gwamna Yari ya bar naira biliyan bakwai don kammala aikin hanyoyin da aka fara a dukkan kananan hukumomi 14 na jihar ba.

A karshe Dosara ya yi kira ga sabuwar gwamnatin ta Bello Matawalle ta yi watsi da zarge-zargen, kar kuma ta yi wa tsohon gwamnan bi-ta da kulli. 

Maimakon hakan ta mayar da hankali domin gudanar da ayyukan ci gaban al’ummar jihar Zamfara.

An dade ana samun sabani da zargin barin bashi ko akasin haka tsakanin gwamnatoci masu barin gado da kuma wadanda suka gaje su a Najeriya. 

A wasu lokutan batun ya kan kai ga shari’a ko kuma ya bude kofar bincike da ma tuhuma daga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kamar EFCC da ICPC.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog