Mahaifi yayiwa ‘yarshi ciki bayan saduwa da ita sau 3

Karatun minti 1

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe ta kame wani magidanci da ake zarginshi da yiwa ‘yarshi ta cikin shi ciki.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai a garin Damaturu,babban birnin jihar.

‘Yan sanda sun kame Muhammadu Hassan bayan zarginshi da saduwa da budurwar diyarshi mai shekaru 22 a duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa budurwar tana dauke da cikin mahaifinta na watanni 5.

Sashin Hausa na LEGIT NG ya rawaito cewa; Mallam Muhammadu Hassan ya sadu da diyarshi har sau 3 bayan ya kwarara mata kwayoyi a abin sha da kosai.

A wani lamarin kuma, rundunan yan sanda ta gurfanar da masu laifi takwas bisa zargin yiwa wasu yan mata tara fyade da kuma yiwa wasu ciki a Damaturu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog