‘Yan Najeriya a shafukan Twitter sun zabi Buhari a matsayin shugaba mafi munin aiki a cikin jerin shuwagabannin da suka mulki kasar.
Zaben da jaridar Sahara Reporters ta shirya a shafin Twitter wanda ya bawa ‘yan Najeriya zabar shugaban kasa mafi muni.
Shafin ya fitar da jerin sunayen shugabannin da suka mulki Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2019 wanda ya hada da Cheif Olusegun Obasanjo, Alh Umaru Musa ‘Yar Adua da shugaba Muhammadu Buhari.
Sau 4 shafin jaridar SAHARA REPORTERS tana shirya irin wannan muhawara a cikin kasa da makonni 2 wanda a kowanne zabe kimanin mutanen da adadinsu yake da yawan gaske.
DABO FM ta binciko cewa a kowacce muhawara shugaba Buhari ne shugaban da aka fi zaba a matsayin shugaba mafi munin aiki a cikin shekara 20.
Sai dai bincikenmu ta nuna cewa shafin SAHARA REPORTERS ta goge sauran muhawarorin da aka tafka, amma duk da haka munyi nasarar samo hotunan wasu daga ciki kamar yadda zaku gani.

