Uncategorized

Burin Mu Shi Ne Samar Da Kwararrun Likitoci-Dr Nuraddeen Umar

Gidauniyar Koyar da aikin kiwon lafiya ta Taufeeq da ke Zariya, ta yaye dalibai 30 da suka yi karatu a fannoni daban-daban tare da kaddamar da 34 da za su yi karatu a sassar wannan makaranta.

Taron, wanda ya gudana a dakin taro na kwalejin Alhudahuda, ya samu halartan Wakilin mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. Dr Shehu Idris, Wanda So Dangin Zazzau Alh. Aminu Mukhtar Sambo ya wakilta, da kwararru a fannin kiwon lafiya da kuma likitanci da sauran iyayen yara.

Da yake gabatar da jawabin sa, Babban Shugaban Makarantar, Dr. Nuraddeen Umar, ya ce, An samar da makarantar ne domin taimakawa gwamnati wurin rage cinkoso a makarantun gwamnati, ta yadda za’a samu adadin dalibai masu yawa da suka kware a fannin kiwon lafiya.

Ya kara da cewa, zuwa yanzu, Makarantar ta yaye dalibai wanda yanzu haka suna aiki a wasu Asibitoci da dakunan karba da shan magani daban-daban a fadin kasar nan.

Sannan, ya yi kira ga daliban da aka yaye su sanya a ransu cewa, kamar yanzu ne suka sa dambar fara gudanar da karatu, domin taimakon al’ummar su da kasar su baki daya.

Da ya juya ta bangaren sabbin dauka kuwa, Nuraddeen Umar, ya bukace su da kiyaye dokokin da bin ka’idojin Makarantar sau da kafa, wanda hakan zai basu damar kammalawa da kyakkyawar sakamako.

Tun farko da yake jawabin sa, Shugaban Makarantar Malam Muhammad Umar, ya godewa iyayen yaran da suke karatu a makarantar ne, saboda gudunmuwar da suke bayarwa domin ci gaban makarantar da kuma karatun yaran su.

Wanda ya yi fatan samun ninkin hakan a sabon zangon karatu da aka fara.

Da yake nashi jawabin, wakilin mai Martaba Sarkin Zazzau wanda So Dangin Zazzau Alh. Aminu Mukhtar Sambo ya wakilta, ya taya daliban da ake yayewa ne murna, kuma ya gode ma malaman Makarantar saboda namijin kokarin da suke ba dare ba rana, domin amfanar da al’umma wasu abubuwa da Allah ya fuwace masu. sannan ya yi kira ga wanda suka amshi rantsuwar fara karatun, su sanya a ransu cewa za su yi ne domin taimakon kai da kai da kuma girmama malaman da za su jagorance su.

Taron ya kawo karshe, da jawabai da bada lambobin yabo, har da kyaututtuka ga wasu daga cikin iyayen al’umma, da kuma ko da yaushe burin su shi ne ci gaban Makarantar.
Kuma an gudanar da wasan kwaikwayo da ya fadakar a kan muhinmancin gwajin jini domin taimakon kiwon lafiyar bil’adama.

Comment here