/

Fashewar abubuwa: Firaministan, Ministoci da ‘yan Majalissu a kasar Lebanon sun ajiye mukamansu

Karatun minti 1

Sakamakon hadarin fashewar wasu abubuwa a kasar Lebanon a makon da ya gabata, Firaministan kasar, Hassan Diab ya ayyana sauka daga jagorantar shugabanci a kasar.

Kazalika wasu daga Ministoci da ‘yan Majalissu a kasar su ma sun sauka daga kan mukaminsu, sun kuma shiga cikin tawagar ‘yan kasar da suke gudanar da zanga-zanga.

Rahotanni daga kasar sun bayyana yadda daruruwan al’ummar kasar sukayi cikar kwari a wani filin da ake wa lakabi da ‘Dandalin Mazan jiya’ domin nuna rashin gamsuwarsu da yadda shugabanni a kasar suka gaza.

An bayyana cewa wasu daga cikin masu zanga-zanga sun yi arangama da jami’an tsaro in da aka harba wa masu zanga-zangar hayaki mai saka hawaye.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog