“A chechi Jama’a” – Aisha Buhari ta shiga cikin masu yi wa Buhari zanga-zanga

Karatun minti 1

Mai ɗakin shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta ƙaddamar da nata goyon bayan akan zanga zangar dake gudana yanzu haka a fadin Najeriya mai taken #Achechijamaa wato “A Chechi Jama’a”.

Dabo FM ta rawaito hakan na zuwa ne bayan Aisha Buhari ta sanya wani bidiyo da yake nuna shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a ciki tare da sauran shuwagabannin tsaro a shafukan ta.

Bidiyon dai na ɗauke da wata waƙa dake bayyana abubuwan dake faruwa a Arewacin Najeriya, “Dan Allah a duba, Arewa na kuka, ana zubar da jinin mu.”

Zuwa yanzu dai kusan jihohon Najeriya suna cigaba da zanga zangar lumana domin kawo ƙarshen matsalolin da suka ddabi ƙasar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog