(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Adamawa: Ni zan fara biyan albashin N30,000, dalibai zasuyi NECO da WAEC Kyauta – Fintiri

Karatun minti 1

Zababben Gwamnan jihar Adamawa, Umar Fintiri ya ce yana daga cikin sabbin Gwamnoni da zasu fara biyan sabon albashin N30,000.

Fintiri ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da manema labarai, yau Juma’a a garin Yola.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Fintiri yace suna nan akan tabbatar wa da mutanen Adamawa alkwawuran da suka dauka a lokacin gudanar da yakin neman zabe.

“Zan inganta tsarin aikin gwamnati, tare da habbaka shi don jin dadin ma’aikata.”

“Saboda inganta tsarin aiki, da gudun shigar ma’aikata yajin aiki, ni zan fara tabbatar da biyan sabon albashi N30,000.”

Fintiri yayi kira ga al’ummar Adamawa dasu kwantar da hankalinsu tare da samun nutsuwa a cigaba da murnar lashe zaben Gwamnan jihar da yayi.

Ya kuma yi kira ga dalibai cewa, a shirin da yake dashi na taimakon bangaren ilimi, ya alkaurantawa dalibai biyan kudin jarabawar kammala sakandire ta NECO da WAEC, domin samun saukin wajen karatun talaka.

“Zamu biyawa dalibai kudin jarrabawar NECO da WAEC domin ragewa iyaye dauyin karatun ‘yayansu.”

Daga karshe ya kuma alkauta cewa bazai ci amanar da mutanen Adamawa suka danka masa ba.

A daren jiya Juma’a ne dai hukumar Zabe ta INEC, ta tabbatar da Alhaji Umar Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa da kimanin kuri’u dubu Arba’in (40,000)

Karin Labarai

Sabbi daga Blog