Copyrighted.com Registered & Protected

Shari’a: Kasar Brunei tayi dokar kisa ga masu aikata Luwadi

Kasar Brunei bisa jagorancin masarautar kasar zata fara aiwatar da dokar hukunci kisa ya masu yin Luwadi, a shirye-shiryen kasar na gyaran wasu kundin tsarin kasar.

Za’a fara aiwatar da kisan ta hanyar jifa da dutse har sai mutum ya rasa ransa.

Tin a  shekarar 2014, kasar Brunei ta kaddamar da Shari’ar musulunci a kasar, bayan hawan Sultan Hassanal Bolkiah.

Tini dai aka fara yankewa wadanda suka aikata laifin sata hannaye.

A kasar Brunei an haramta shan giya tare da hukunta duk wanda aka kama baya sallah musamman ta Juma’a.

Hukunci zai tabbata akan musulman kasar ne kawai.

%d bloggers like this: