Labarai

Addinin kirista na koyar da zaman lafiya da son juna-most Reverend Ali Buba Lamido

Shugaban Darikar Angalican communion diocese na wusasa Most Reverend Dr. Ali Buba Lamido, ya shawarci gwamnatin tarayya ta yi amfani da rufe kan iyakokin kasar nan ta kasa da ta yi, wurin kakkabe masu tayar da kayan baya. wanda ya kwatanta su a matsayin wadanda ke shigowa daga kasashe makofta domin aikata ta’addanci a nan cikin gida najeriya.

Ya bayyana haka ne, sa’ilin da yake gabatar da jawabin sa na shekara-shekara a taron Majalisar kiristoci mabiya Darikar Angalican da ya gudana a kauyen Mai-mai dake Gundumar Gwanki a Karamar Hukumar Makarfi.

Ya ce, ya zama wajibi a yabawa kokarin da gwamnatin shugaban kasa Buhari ke yi ta fuskacin yaki da miyagun mutane da suka addabi Al’umma, kuma suke kai hare-hare babu ji babu gani, Amma da bukatar gwamnatin ta dada karawa akan kokarin da take.

“Muna kuma yabawa gwamnatin Jihar Kaduna, saboda irin ayyukan more rayuwa da take yi, Gwamnati ta damu matuka da matsalar tsaro da ake fama da shi, wanda masu tada tarzoma suke tada ita, sai dai muna kira ga gwamnatin ta yi amfani da kimiyya wurin gano maboyar ‘yan ta’addan kuma a gurfanar da su” inji Dr Ali Buba Lamido.

Ya shawarci mabiya addinin kirista, su kasance masu biyayya ga abun da Allah madaukakin Sarki ya tsara, kuma a yiwa Shuwagabanni biyayya ta yadda za’a samu rayuwa mai kyau.

Da ya juya ga taken bukin na bana kuwa, Most Reverend Dr Ali Buba, ya yabawa daukacin mabiya Darikar Angalican communion diocese wusasa ne saboda yanda suke aiki ba dare ba rana domin cigaban cocin, musamman mata da matasa da ya kwatanta a matsayin kashin bayan cigaban kowacce Al’umma.

Ya ce, zuwa yanzu sun samu gagarumar nasara wurin cika wasu daga cikin muradun cocin, da suka hada da biyan albashin ma’aikatan da suke aiki karkashin sa da kokarin fara gina gida na musamman ga limaman cocin da suka yi ritaya, da kara inganta Asibiti da makarantu dake karkashin cocin da kuma koyar da Matasa maza da mata sana’o’i na dogaro da kai da zai rage zaman kashe wando tsakanin su.

A cewar sa, addinin kirista na koyar da zaman lafiya da son juna da kuma gyara alakan dake tsakanin mabiyan sa a ko’ina suke, shiyasa ma basu kasa a gwiwa wurin kyautata sha’anin ilimi a bangaren su.

Daga nan sai ya yi fatan samun dawwamammen zaman lafiya a kasa baki daya.

Karin Labarai

UA-131299779-2