Labarai

Ta’addanci: Duk randa Abdulaziz Yari ya sake zuwa Zamfara, da kai na zan kama shi – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana shirinshi na kama tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari.

Hakan na zuwa ne bayan da Gwamna Matawalle ya zargi tsohon gwamna da tayar da zaune tsaye a cikin jihar duk da irin kokarin da yace gwamnatin jihar take yi a yanzu domin samun zaman lafiyar jihar.

Da yake jawabi a yayin taron mika wuya da wasu ‘yan Bindiga suka yi, Matawalle ya bayyana cewa duk a lokacin da Abdulaziz Yari ya shigo jihar, yana tara mafarauta a gidanshi domin su tattauna.

Ya kuma tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana barin jihar, mafarautan suka farwa jama’ar gari da ayyukan ta’addancin da suka saba.

“Daga yau, idan muka kuma jin tsohon gwamna ya shigo ya fita an samu matsala, wallahi zan kamashi da hannu na.”

“Ya sani (Abdulaziz Yari) cewa na fishi rashin kunya idan ita yake ji.”

DABO FM ta tattaro gwamnan a yayin da yake tabbatar da cewa; “Zuwanshi na 3 kenan zuwa jihar Zamfara, duk randa yazo sai an samu matsala kuma a ranar yake guduwa ya tafi bayan ya gana da mafarauta da barayi.”

“Na kirashi, kada ya sake zuwa Zamfara akan wannan.”

Tin dai bayan darewar gwamnan Matawalle mulkin jihar, zaman lafiya jihar ya samu tagomashi tare da dimbin nasorori kamar yacce masu bincike suka tabbatar.

Sai dai duk da haka wasu na ganin gazawar Gwamnatin da ta dauki salon sulhu da yan Bindigar maimakon tayi kokarin murkushe su.

Karin Labarai

Masu Alaka

Abdulaziz Yari ya mikawa Matawalle takardun mulkin jihar Zamfara

Dabo Online

“Kuna kan gwaji na wata 3” -Gov Matawalle ga sabbin Kwamishinoni da Masu Bada Shawara

Muhammad Isma’il Makama

Bayan biliyan 1 na gyaran makabartu, Matawalle zai gina sabon gidan gwamnati na biliyan 7

Dabo Online

A kalla ‘Yan Gudun Hijira 25,000 suka koma Gidajensu na ainahi a jihar Zamfara

Dabo Online

‘Yan Bindiga da dama a Zamfara sun zubar da makamansu tare da neman yafiya – Matawalle

Dabo Online

Zamfara zata fara noman kwakwar man ja – Matawalle

Dabo Online
UA-131299779-2