Ahmad Lawan ya lashe zaben shugaban majalissar Dattijai

Karatun minti 1

Sanata Ahmad Lawan ya lashe zaben shugaban majalissar dattijai a zaben da aka gudanar yau Talata.

Bayan an kammala zaben, magatakardar majalissar ya sanar da Sanata Ahmad Lawan a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sanatoci 107 ne suka kada kuri’a gabaki daya inda Ahmad Lawan ya samu 79, Ali Ndume ya samu 28.

Adadin Kuri’u; 107

Ahmad Lawan – 79

Ali Ndume – 28

Karin Labarai

Sabbi daga Blog