Labarai

Aisha Buhari ta haramta wa shugaba Buhari haduwa da kowa

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta haramtawa shugaban haduwa da kowa inda tace ya zauna a gida.

Hakan na zuwa ne bayan tabbatar da cutar a tare da babban makusancin shugaban kuma shugaban ma’aikatan gwamnatin Najeriya, Mallam Abba Kyari.

DABO FM ta tatttara cewar jaridar ThisDay da rawaici cewar an tabbatar da samun cutar a jikin Mallam Abba Kyari bayan gwajin da akayi masa tare na cutar COVID-19 jim kadan bayan dawowarshi daga kasar Jamus.

Sai dai gwajin shugaba Buhari akan cutar ya nuna shugaban ba ya dauke da cutar.

Daily Nigerian ta bayyana cewar “Aisha Buhari tayi wa shugaba Buhari katanga da kowa, ta hana shi zuwa ofishinshi domin gudanar da ayyukan.” – kamar yadda wata majiya a fadar gwamnatin ta bayyanawa jaridar.

Karin Labarai

UA-131299779-2