Labarai

Yanzu-Yanzu: Jami’an tsaro sun garkame Majalissar karamar hukumar Zariya

Mu’azu Abubakar Albarkawa

Zaria, Kaduna.

Bayan rahotannin da Dabo FM ta ruwaito a kwanakin baya game da rikicin shugabancin da ya barke a majalisar kansilolin karamar hukumar Zariya a ihar Kaduna, yanzu haka a Talatar nan jami’an tsaro da suka hada da ‘Yan sanda da Civil Defence da kuma ‘yan banga, sun killace majalisar tun da sanyin safiya.

Zagayen da Dabo FM ta yi a wurin, ya gano yadda aka girke Jami’an da yawan su ya kai 25 zuwa 30 kuma suke killace da majalisar.

Sai dai mun tsinkayi wasu gungun kansilolin da yawan su ya kai 7 tsugune a wani masallaci da ke kusa da majalisar.

Duk da ba su yarda an nadi muryar su ba, sun bayyanawa manema labarai cewa, suna zargin bangaren dakataccen shugaban majalisar da yake ikirarin bai dakatu ba Hon Hashimu Bako, da hannu wurin sanya Jami’an tsaron su killace majalisar ba shiga ba fita.

Kuma sun bayyana yadda aka hana su shiga majalisar tun da suka zo da misalin karfe 10 na safiya.
A bangare guda kuma, sun nuna shakku kan akwai wata boyayyiyar manufa na zaman majalisar, kasancewar suna da labarin cewa an baiwa wancan bangaren sabon sandar gudanarwar majalisar.

Sai dai da Dabo FM ta tuntubi bangaren Hon Hashimu Bako, ya ce, baida masaniya a kan turo jami’an tsaron kuma yanzu haka maganar da yake yana garin Kaduna domin gudanar da wani aiki da ya shafi majalisar.

Bisa zargin jin rade-radin zaman majalisar kuwa, ya ce, shi bai san da wannan maganar ba.
“Kuma kace sun ce sun ji rade-radi, to tunda sun ji rade-radi, idan za’a yi zaman majalisa rade-radi suke ji ko kuma text ake ake masu”, inji Hashimu Bako

UA-131299779-2