//
Sunday, April 5

Gwamnatin Kano ta musanta shigar da Corona Virus cikin jihar ta filin Jirgi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ggwamnatin jihar Kano ta barranta daga wasu labarai dake yawo a shafukan sada zumunta kan cewar an an shigar da Corona Virus cikin jihar ta filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano.

DABO FM ta tattara cewar wani faifan bidiyo ya nuna yadda jirgin kamfanin Air Peaace yayi carko-carko a filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano. Mutane sun zargi cewar matukin jirgin yaki bude jirgin saboda zargin akwai mai dauke da cutar Corona Virus.

A jawabin mataimakin shugaban kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa na yaki da cutar, Farfesa Abdulrazak Habib yace ba’a shigo da cutar ba domin gwaje-gwajen da sukayi wa matashin baya dauke da cutar a dalilin haka ne yasa suka sallameshi.

Masu Alaƙa  Yanzu yanzu: An samu karin mutum 20 masu dauke da Coronavirus, jumilla 131 a Najeriya

Sai dai wasu rahotanni sunce wani matashi ne mai shekaru 17 yayi amai a lokacin saukar jirgin wanda shine dalilin tsaida jirgin.

Haka zalika, daya daga cikin mataimakan gwamnan jihar a fannin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, zance da ake fada yayin yada bidiyon ba gaskiya bane.

“Bidiyon da ake yadawa na jirgin Airpeace da ake cewa an samu mai cutar COVID-19, ba haka zancen yake ba.”

“Matukin jirgin yaki yarda ya bude kofar jirgin yayin da suka sauka a Kano bayan ya samu labarin daya daga cikin fasinjojin jirgin yayi amai a lokacin da suke sama.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020