Copyrighted.com Registered & Protected

Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta bude iyakoki don cigaba da safarar motoci – Ali

Shugaban hukumar hana fasakauri ta Najeriya, Kwastam, Hameed Ali, yace akwai yiwuwar gwamnatin shugaba Buhari ta bude iyayokin shigowa da motoci cikin kasar ta kan titi.

Tin dai a watan Janairun 2017 ne gwamnatin ta saka dokar data hana shigowa da motoci cikin kasar ta kan titi.

Gwamnatin ta hana shigowa da motocin da kan titi ne jim kadan bayan daka saka dokar hana safarar shinkafa a watan Afrilun 2016.

Yace rundunar ta saka dokar ne domin kididdigar gane dukkanin motoci da sauran dangoginta dake shigowa cikin kasar, kuma sunyi nasara.

Hameed Ali, yace gwamnatin zata yi duba da kuma yiwuwar cire takunkumin da hukumar Kwastam ta kakaba.

Masu Alaƙa  Ku taimaka, ku daina cin Shinkafa 'yar kasar waje, tana dauke da Guba - Shugaban Custom

“Idan aka shigo da motoci ta iyakar titi, bamu da bayan yadda motar ta shigo cikin kasa saboda sunayin takardun bogi, wannan shine ya zama ruwan dare.

“Anyi dokar ne dama saboda a samu ikon kula da kuma dakatar da aikata haka.”

Masu alaka

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: