Dalibi ya rasu kwana daya bayan kammala karatu da ‘First Class’ a BUK

Karatun minti 1

Al’amin, dalibi a jami’ar Bayero dake jihar Kano, ya rasu kwana daya bayan daya kammala digiri da babban sakamakon ‘First Class.

Alamin ya kammala karatunshi a sashin ‘Banking and Finance’.

Kwana daya kafin rasuwar Al’amin, ya aike da sakon taya murna ga abokanshi tare da basu uziri dalilinshi daya saka bai halarcin taron bikin kammala karatun nasu ba.

Bayan tattaunawar mu da wasu daga cikin abokanshi, Baffa Tijjani, ya shaida mana cewa, Al’amin ya shaida musu bazai samu damar zuwa ba, bisa wata yar gajeriyar tafiya da yayi inda daga nan ne kuma ya kamu da rashin lafiya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog