Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Akwai yiwuwar samun sabuwar Boko Haram idan ba’a saki Sheikh Zakzaky ba – Majalissar tarayya

2 min read

Majalissar Dattijan tace zanga-zangar da kungiyar takeyi ta fara haifar da mara ido.

Majalissar ta bayyana haka ne a zaman ta na ranar Laraba, inda ta bayyana cewa cigaban zanga-zangar mabiya Shi’a zai iya haifar da fitina.

‘Yan kungiyar Shi’a suna yin zanga-zangar ne domin neman gwamnatin tarayyar ta saki shugaban kungiyar, AL Sheikh Zakzaky tin bayan shekaru da suka gabata.

An tsare El Zakzaky ne bayan da ‘yan kungiyar su kayi arangama da tawagar Shugaban hafsoshin kasa na Najeriya, Tukur Buratai a shekarar 2015.

Kotuna daban daban sun baiwa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari umarnin saki tare da bayar da belin Al Zakzaky, inda mabiya shi’a suke kiran gwamnatin ta mai kunnen kashi.

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito cewa “A yayin zaman majalisar, shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya gabatar da wata kudiri na kira ga takwarorinsa su gudanar da bincike kan lamarin da kuma kara inganta tsaro a majalisar.

Yayin da wasu ‘yan majalisar suka goyi bayan inganta tsaron wasu sun jadada cewa ya dace a binciko ainihin matsalar wadda itace cigaba da tsaren El-Zakzaky.

Sun bayyana cewa irin wannan lamarin ne ya haifar da kungiyar Boko Haram a Najeriya.

Onofiok Luke daga Akwa Ibom ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin tarayya ke kin bin wasu dokokin kotu na sakin El-Zakzaky.

“Idan har kotu ta ce a sake shi, ya kamata mu bukaci gwamnati ta sake shi. Ba batun kutsen da akayi a majalisa bane abinda ya kamata mu rika tattaunawa.”

Bamidele Sam daga jihar Osun ya ce cigaba da tsare El Zakzaky rashin adalci ne kuma idan aka yi wa mutum daya rashin adalci abin ya shafi kowa.

“Ina kira da gwamnatin tarayya da sake duba batun shugaban kungiyar … ta bari doka ya yi aikinsa … domin kaucewa samuwar sabuwar Boko Haram daga kungiyar Shi’a,.” 

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.