APC tayi rashin nasara bayan kotu ta tabbatar da Darius Ishiaku na PDP a matsayin halastaccen gwamnan Taraba

Kotu dake sauraron kararrakin zabe tayi watsi da karar Abubakar Danladi, dan takarar gwamnan jihar Taraba, ya shigar gaban kotun dake da zamanta a birnin tarayyar Abuja.

Abubakar Danladi ya shiga kotu ne bisa kalubalantar nasarar zaben gwamnan jihar, Darius Ishiaku.

Tin a wata 5 ga watan Yuli, kotun koli ta kara zartar da hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke na korar karar Danladi bisa karyar shekarun haihuwa.

Shima nashi hukuncin, mai shari’a M.O Adewarahe ya bayyana cewa dole ne kotun zaben tayi watsi da karar biyo bayan hukuncin da kotun koli tayi na korar karar dan takarar jami’iyyar APC tare da tabbatar da jami’iyyar PDP da gwamnan jihar Ishiaku Darius a matsayin wadanda suka lashe zaben jihar.

Tawagar alkalan wannan kotun ta zabe ne suka yi watsi da wannan kara, bayan sunyi la’akari da hukuncin Kotun koli ta kasa. A karshe dai sun yi watsi da karar kasancewar Danladi Abubakar ya yi amfani da shekarun karya.

Masu Alaƙa  Kotu ta cire sunan Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na jami'iyyar PDP

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: