Labarai

Al’ajabi: An kama wani dan Najeriya ya dane kan jirgin saman da zaije turai

Hukumomin filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake garin Ikko sun samo nasarar damke wani dan Najeriya da ya dane kan jirgin Peace Air domin zuwa turai.

Majiyar Dabo FM ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda saurayin dan kimanin shekaru 25 yayi kokarin makalewa a jirgin wanda ya bayyana da cewa ya dauka jirgin kasar waje ya nufa.

Hukumomin kamfanin jirgin sama na Peace Air ya bayyana cewa wani babban kaftin din jirgin sama wanda ba na haya ba ne ya gano wannan saurayi, a dai dai lokacin da yake jiran tashin jirgin na kamfanin Peace Air shi kuma yana kokarin tashi cikin jirgin da yake tukawa.

Shugaban hukumar tashin jirage ta Najeriya, Mista Henrieta Yakubu ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Karin Labarai

UA-131299779-2