Labarai

Iyayen Sulaiman sun gindaya sharudan da Baturiya zata cika kafin ta auri ‘dansu

Iyayen matashin nan dan jihar Kano da baturiyar Amurka tayi tattaki zuwa gidansu domin suyi aure, sun gindaya sharudan da zata cika kafin su aura mata ‘dansu.

A dai cikin makon nan dai baturiyar mai shekaru 43 yar kasar Amurka ta isa zuwa jihar Kano bayan narkewa a cikin soyayyar matashi Sulaiman mai shekaru 23 da suka hadu a manhajar Instagram.

DABO FM ta tattara cewa tini dai aka sanya watan Maris a matsayin lokacin da za’a yi bikin masoyan gida biyu bayan amincewar iyayen matashin dake zaune a unguwar Panshekara ta jihar Kano.

Sai dai daga bangaren mahaifin matashin wanda yake tsohon jami’an dan sanda, Alhaji Isa Sulaiman, yace za’a saka hukuma a cikin lamarin.

Haka zalika, jaridar Kano Focus tace mahaifin matashi Sulaimanu ya gindayawa baturiya, Mis Jannie Sanchez, sharudan da zata cika kafin ya amince a daura auren harma ta koma dashi kasar Amurka.

Sharudan sun hada da, samun shaidar daga jami’an tsaro, wanda ya tabbatar da cewar a ranar Litinin, zai garzaya zuwa ofishin hukumar tsaro ta farin kaya ‘DSS’.

Ya kara da cewar; ‘danshi zai cigaba da karatunshi a kasar Amurka idan sun tafi tare da barinshi akan addininshi na Musulunci.

A cewar Mis Jannie, ta karbi sharadin inda ta tabbatar cewar akwai yiwuwar ta karbi addinin Musulunci.

A karshe, kamar yadda KANO FOCUS ta tabbatar, mahaifin Sulaiman yace bazai aura mata ‘danshi ba tare da sahalewar iyayenta ko shakikanta ba, wanda a cewarshi ya sabawa koyarwa addinin Islama.

Tini dai Misis Jannie ta amince da dukkanin sharudan inda ta bayyana zata koma Amurka domin kammala shirye-shirye kafin lokacin auren da aka sanya yazo.

Karin Labarai

UA-131299779-2