//
Wednesday, April 1

Ali Jita ya raba wa ‘Almajirai’ rigunan sanyi da barguna

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Fitaccen mawakin Hausa na zamani, Ali Isa Jita wanda aka fi sani da Ali Jita, ya jagoranci rarrabawa ‘Alamjirai’ riguna na sanyi a jihar Kano.

Da yake bayyanawa a shafinshi na manhajar Instagram, mawakin ya nuna jin dadinshi bisa ga rabawa ‘Almajiran’ kayayyakin.

Da yake tabbatar da lamarin, Ali Jita, ya shaidawa DABO FM cewar ya raba kayayakin a unguwar Darmanawa dake jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewa mawakin tare da abokinshi, Darakta Manga Muhammad sun rarraba kayayyakin da suka hada da rigunan sanyi, kayan sawa da abinci.

Yace; “Alhamdulillah, yau mun bi layi layi, mun rarraba kayan sawa, abinci da barguna.”

Masu Alaƙa  Yacce yan matan Kannywood suka shilla yawan shakatawa a manyan biranen duniya

Da yake mayar da martani bayan wani ya soke shi kan cewar; “A dena daukar hotunan wadanda ake taimakawa”, mawakin yace ba suna yi bane domin neman duniya ta sani, illa iyaka sunayi ne da nufin zaburar da wadanda basu da niyyar yi.

“Bama yin wannan abin don mu burge wani. Mu mutane ne da muke burge wasu, kuma sukan kwaikwayi duk abinda mukeyi, don haka munayi ne domin masoyanmu suyi irin yacce mukeyi.”

“Ka taimaki mutum daya, wannan wanda ka taimaka zai iya taimakon mutum miliyan.

A wani labarin shima, Darakta Hassan Giggs, ya daukin nauyin yi wa wani matashin aiki ido bayan makancewarshi a shekarar da ta gabata.

Masu Alaƙa  Shugaban Majalissar Dattijai ya baiwa jarumi Mustapha Nabruska mukami

Itama jaruma Rahama Sadau ta rarraba kayayyakin sanyi ga Almajiran a ranar 8 ga watan Janairun 2020.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020