Engr Saleh Mamman, Ministan lantarkin Najeriya.
Labarai

Minsitar Lantarki ya bayyana dalilan rashin samun tsayayyar wuta

Ministan Lantarki , Injiniya Sale Mamman yace ana samar da isasshiyar wautar lantarki tare da cewar harkokin tura wutar lantarkin ya samu cigaba.

Sai dai ministan ya bayyana cewa ana samun matsalar rashin lantarkin ne wajen rarrabata wanda matslar kasuwanci yake haifar wa.

“Rarraba wutar lantarki, har yanzu shine matsalar saboda asarar masu kasuwancinta da kuma matsalolin na’urori. Fatan a wannan shekarar shine samar da karfin lantarki na 7000, zuwa 2023 kuma zamu samu karfin 11,000.

“Daga lokacin kamfanin Siemans ya gama aikinshi, za’a samu cigaba. A yanzu haka muna da wutar da yawanta ya kai ‘megawatt’ 14,000 amma 4,500 muke sarrafawa wanda a haka muna iya raba 3,700 ne kadai daga abinda muke dashi. Suma kamfanunuwan rarraba wutar lantarkin suna iya biyan ta ma’aunin 1,400 ne kacal.”

“To kunga inda matsalar take.”

Karin Labarai

UA-131299779-2