0
Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Shaikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina tare da Babban Daraktan Hukumar, Dakta Aliyu Musa Aliyu a safiyar yau Juma’a sun baje kolin yammata 32 ta suka damke suna yawon ta zubar a kwararo na jihar Kano.
Dabo FM ta hada muku rahoton ne yayin da shugabannin hukumar ke zagaye domin duba matan da aka kama a yayin wani sumame da Dakarun Hisbah suka gabatar a daren jiya Alhamis inda aka kamo Mata har guda 32.
Babban Kwamandan Hisbah ya yi musu nasiha mai ratsa jiki, yayin da kuma ake ci gaba da bincike a kansu domin gayyato iyayensu kuma a ga matakin da ya dace na Shari’a a kansu. Kamar yadda Hukumar ta wallafa a shafukan ta.
