Labarai

Alkalin alkalan Najeriya ya dakatar da shari’ar zaben gwamnoni na wucin gadi

Alkalin alkalan Najeriya ya dakatar da cigaba da sauraron daukaka karar zabubbukan gwamnoni da ake gudanarwa a yanzu haka.

Dakatarwar tazo ne biyo bayan cunkuso da tururuwan mutane da suka shiga cikin zauren kotun.

Alkalin ya bayar da umarnin ficewar kowa daga zauren, banda lauyoyin masu kara da wadanda ake kara tare da su masu karar da wadanda ake kara.

A yau dai ake sa ran kawo karshen shari’ar jihohi 7, a zaben gwamnan da aka kammala ranar 9 ga watan Maris na 2019.

Tin dai karfe 6 na safe, magoya bayan gwamnonin jihohin Kano, Sokoto, Bauchi, Adamawa, Imo Binuwai da Filato suka cika dakin kotun.

Cikakken bayanin na zuwa…

Karin Labarai

UA-131299779-2