//
Wednesday, April 1

Alkalin alkalai ya sake dakatar da shari’ar Abba da Ganduje

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rahotannin da suke shigowa yanzu daga babbar kotun Najeriya, Daily Trust ta bayyana cewar alkalin alkalai ya dakatar da shari’ar gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje da Abba Kabiru Yusuf na PDP.

DABO FM ta tattara cewar wannan ne karo na 2 da alkalin, Tanko Muhammad, yake dakatar da shari’ar.

A karo na farko, ya dakatar da shari’ar ne bisa hayaniyar mutane da suke cikin zauren Kotun.

A wannan karon, CJN Tanko Muhammad ya dakatar da shari’ar ne bisa rashin lafiyar da ba’a bayyana kowacce ba da take damun daya daga cikin alkalan dake sauraron shari’ar.

Cikakken bayanin na zuwa….

Masu Alaƙa  Kotu ta kwace zaben ‘Yan Majalissun jiha guda 2 daga APC ta baiwa PDP a jihar Adamawa

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020