Allah Yayi wa fitaccen dan jarida Umar Sa’idu Tudun Wada rasuwa

Karatun minti 1

Fitaccen dan Jarida, tsohon shugaban rukunin tashohin gidan Rediyon Freedom dake jihar Kano, Alhaji Umar Sa’idu Tudun Wada ya rasu a yau Lahadi.

Alhaji Umaru ya rasu ne sakamakon hatsarin mota daya ritsa da shi a kan hanyarshi ta dawowa daga garin Abuja kamar yacce gidan Rediyon Freedom ya bayyana.

Yayi hatsari ne a garin Kura, dai dai lokacin daya rage masa saura kilomita kasa 27 ya karasa tsakiyar birnin Kano.

Muna addu’a Allah Ya Kyauta Makwancin shi.

Tin bayan fara aikin jaridarshi a gidan Talbijin na CTV dake Kano a shekarar 1981, Marigayi Alaji Umaru Tudu Wada, ya rike shugaban gidan rediyon jihar Kano (Radio Kano) da gidan rediyon Freedom. Ya kuma yi mai bawa tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, shawara a fannin yada labarai.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog