(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

2020: Rikici ya barke a APC tsakanin Oshiomhole da Gwamnan jihar Edo akan fitar da ‘yan takara

dakikun karantawa

Sabon rikicin cikin gida na jami’iyyar APC ya barke tsakanin gwamnan jihar Godwin Obaseki da shugaban jami’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomole.

Rahotanni sun bayyana tuni dai jami’iyyarta rabe gida biyu inda wasu ke bin tafiyar gwamnan jihar, wasu kuma suke tafiyar shugaban jami’iyyar na Kasa.

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito cewa; “Tsohon gwamna Adams Oshiomhole ne ya yi ruwa da tsaki wajen ganin Godwin Obaseki ya gaje sa. Daily Trust ta rahoto cewa da farko gwamman na yanzu, bai cikin masu neman takara a wancan lokacin.

Godwin Obaseki ya na hawa kan mulki ya hana wadanda su ka maida gidan gwamnatin jihar Edo wajen yawo shiga ganin gwamna.

Bayan nan kuma sabon gwamnan ya fara ware yaran babban Maigidan sa a gefe. Gwamna Obaseki ya nunawa Mutanen Adams Oshiomhole cewa kudin gwamnati na jiha ne, har ta kai ya fara sauke wasu daga cikin Yaran tsohon gwamnan daga kan manyan mukaman da su ke rikewa a jihar.

Ba a nan rikici ya tsaya ba, domin kuwa sai da ta kai an soke zaben fitar da gwani na kujerun majalisa da APC ta fara shiryawa bara a jihar Edo.

Wannan ya sa rikicin Oshiomhole da Magajin na sa ya fito fili. An kuma gwabza a majalisa tsakanin wadannan bangarori biyu. Kwanaki a ka tsige Kakakin majalisar dokoki, a ka maye gurbin su da wanda gwamna ya ke so, daga baya, a ka sake tsige sabon da a ka nada.

Wannan rikici na majalisa bai kare ba tukuna a wannan gwamnati. A 2020 ne za a zabi sabon gwamna. Masana siyasa su na ganin Obaseki zai iya samun tikiti ta hanyar wasu manyan APC da ke tare da shi har gobe.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog