Babban Labari Labarai

Al’ummar Kaduna na cikin mawuyacin hali – Mustapha Adamu Ubaidu

A sakon sa na barka da sallah da taya al’ummar musulmi murnar kammala Azumin watan Ramadana lafiya, wani uban kasa a masarautar Zazzau, Marafan Yamman Zazzau Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullahi, ya roki Allah kada ya mai-maita wa al’umma halin da aka shiga a sallar bana saboda cutar sarkewar numfashi ta Covid-19.

Marafan Yamman Zazzau, ya bayyana haka ne da yake zantawa da Dabo FM a Zariya.

Ya ce, duk da an kammala Azumi lafiya, amma halin kuncin da al’umma musamman wanda ba su da cin yau ballantana na gobe suka shiga, akwai bukatar al’umma su koma ga Allah madaukakin Sarki su naimi yafiyar sa dalilin zunuban da ake aikatawa na yau da kullum.

Ya bukaci shuwagabanni musamman masu jagoranci su ji tsoron Allah akan dukkanin abubuwan da suke aikatawa kasancewar dole a rika lura da rayuwa da dukiyoyin al’umma.

Kuma su tuna rantsuwar da suka yi da Al-qur’ani game da jagoranci al’umma.

Da ya juyo ga Jihar Kaduna kuwa, Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullahi, ya kwatanta matakan da gwamnatin ta dauka a matsayin wanda sam basu dace ba, kuma a maganar gaskiya an cuci al’umma akan tsarin da ake kai.

Yau a Jihar Kaduna, al’umma na cikin halin kuncin maras musaltuwa game da kullen da aka yi, amma ya roki Allah rahimin Sarki ya kawo mafita.

Sai dai duk da haka, ya shawarci al’umma su cigaba da bin ka’idojin da aka sanya domin inganta lafiyar su.

Ya taya Mai Martaba Sarkin Zazzau kuma shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kaduna da al’ummar masarautar Zazzau da Jihar Kaduna da kuma Najeriya baki daya murna, saboda ganin karamar sallar bana.
Sannan ya roki Allah ya mai-maita cikin koshin lafiya da aminci.

Karin Labarai

UA-131299779-2