A dai-dai lokacin da ake cigaba da bukuwan sallah karama, wani dan siyasa kuma basarake a masarautar Zazzau Alhaji Sama’ila Musa Sarkin Gandun Zazzau, ya yabawa matakan da gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka domin dakile yaduwar cutar sarkewar numfashi ta Covid-19, musamman ta fuskar takaita zirga-zirgan Jama’a domin lalubo hanyoyin kawar da cutar daga Jihar.
Sarkin Gandun Zazzau, ya bayyana haka ne a wata tattaunawar da ta hada shi da manema labarai ciki kuwa har da Dabo FM a Zariya.
Ya ce, kokarin abun a yaba ne matuka, saboda lokacin da gwamna El-rufa’i ya dauki wannan matakin wasu jihohi sun gaza fahimtar matsalar sakin mutane su cigaba da zirga-zirga kuma ga cutar na karuwa.
Inda ma ya shawarce shi ya kara inganta hanyoyin da yake bi saboda rantsuwa ya yi da Al-qur’ani zai kare lafiya da dukiyoyin al’ummar sa.
A cewar Alhaji Sama’ila Musa, wasu da dama musamman wasu malamai sun sanya siyasa a jawaban su daban-daban lokacin Tafsirin Al-qur’ani mai girma na azumin bana, Sai dai sun gaza fahimtar Allah ne ya ba Malam Nasiru El-rufa’i jagoranci da har suke adawa da hakan.
Ya shawarci al’umma da sauran masu adawa da wannan matakin su mayar da wukar cikin kube, kuma su zo a hadu a hada karfi da karfe domin ceto al’umma.
Da ya juya ga bukin sallar karama na bana kuwa, Alhaji Sama’ila Musa, ya taya Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris murnar kammala Azumi lafiya, kuma ya yi fatan samun dawwamammen zaman lafiya a lardin Zazzau Jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya
