Wasanni

An samu raunuka da dama bayan farwa magoya bayan Kano Pillars a Katsina

Wasu fusatattu matasa da ake zargin magoya bayan kungiyar kwallon kafan Katsina United ne sun tsare yan wasa da ma’aikatan kungiyar na tsawon awanni bayan tashi daga yin canjaras a jihar Katsina.

Kano Pillars, kungiya da take kan mataki na 13 akan teburin kwallo ta ajin kwararrun Najeriya, ta buga wasan mako 15 inda Kungiyar kwallo ta Katsina United ta karbi bakuncinta.

Sai dai wasan da aka buga a filin wasa na Muhammadu Dikko ya tashi da hargitsi, inda aka zargi magoya bayan Katsina United da afkawa magoya bayan kwallon kafa ta Kano Pillars.

DABO FM ta tattara cewar yan wasan Kano Pillars sun kasa fita daga filin wasan zuwa wajen zama na hutun rabin lokaci bisa tsoron kada a cin musu yayin da suka shige ciki duk da yawan jami’an tsaron dake a cikin filin.

Daily Trust ta tabbatar da cewa, magoya bayan Katsina United sunyi tururuwa wajen hana yan wasan Kano Pillars ficewa daga filin.

An samu rikici tsakanin magoya bayan Kano Pillars da Katsina United wanda ya kai ga samun raunuka masu tsanani. Daga bisani, yan wasan Kano Pillars sun samu ficewa daga filin bisa rakiya jami’an tsaro.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, mai yada labaran kungiyar Kano Pillars, Lurwanu Idris Malikawa Garu, yace hakan ya tilastawa Kano Pilllars sauya hanyar komawa gida bayan samun rahotannin magoya bayan Katsina United sun tare musu hanya.

An dai tashi wasan ne canjaras, 1-1.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kano Pillars ta lashe kofin Aiteo na shekarar 2019

Dabo Online

Kano Pillars ta lallasa Jigawa Golden Stars da ci 2 da nema

Dabo Online

LMC ta dakatar da Rabi’u Pele na Kano Pillars, wasanni 12 bisa yunkurin yiwa alkalin wasa dukan kawo wuka

Dabo Online

Anci tarar Kano Pillars miliyan 8 bisa janyo rigima ana tsaka da wasa a jihar Legas

Dabo Online
UA-131299779-2