Labarai

An cuci mutanen Zamfara kuma Allah zai bi musu hakkinsu – Abdulaziz Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari yace “An cuci mutanen Zamfara, kuma Allah zai isar musu.”

DABO FM ta binciko wani bidiyo da Mai Biredi TV ta wallafa a shafinta na Facebook yayi wata ziyara da tsohon gwamnan ya kaiwa ‘ya yan jami’iyyar APC na jihar.

‘Yan uwa na, yan jami’iyyar APC na jihar Zamfara, wandanda sukazo mana barka da zuwa bayan mun gama aiki. Ina godiya kwarai, Allah ya saka muku da alkhairi.”

Yari, yayi kira ga ‘ya yan jami’iyyar da su kwantar da hankalinsu kuma su kara hakuri game da karbe mulkin jami’iyyar da kotu tayi da baiwa PDP.

“A kara hakuri, abinda aka gani, ba wanda zai iya yinshi inba Ubagiji ba, duk abinda ake gani a barshi a matsayin jarrabawa ta Ubagiji.”

Nayi iyakar yi na domin kyautatawa a cikin jagorancin shekara 8 da Allah ya bani.”

Ya kara kira da mutane da su kwantar da hankalinsu domin a yanzu shirye-shiye sunyi nisa wajen fafutukar dawo musu da hakkinsu.

“Ba iya Najeriya ba, duk duniya an yarda cewa da an zalunci al’ummar jihar Zamfara, wannan hakkin in Allah Ya yarda, ba da zimawa zai dawo.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Bana cikin taron hadin kan APC na ‘Babba-da-Jaka’ da Yari ya kira -Sanata Marafa

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2