Home LabaraiNi ba Dalar da zaka saka a Aljihu ba kunya bane – Martanin Wike ga Ganduje akan rushe Masallaci

Ni ba Dalar da zaka saka a Aljihu ba kunya bane – Martanin Wike ga Ganduje akan rushe Masallaci

by Dabo Online
0 comments

Ayi hakuri da yawan Talloli – Dasu ne muke gudanar da ayyukanmu.

Gwamnan jihar Ribas, Nysoem Wike, yayiwa mai girma gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje martani akan maganarshi ta cewa zai maka Wike a kotu.

Ranar Asabar ne gwamnan jihar Kano ya fitar da sanarwa yana kiran mutane da su kwantar da hankulansu akan rushe Masallacin domin zasu dauki duk matakan da suka dace.

Sai dai gwamnan jihar Ribas, ta hannun kakakinshi, Simeon Nwakaudu, yayi kakkausar martani ga gwamna Ganduje.

Ya bayyana cewa; Gwamna Ganduje ya kwana da sanin cewa shi ba Dalar da zai iya sawa a Aljihu bane babu kunya ba tsoron abinda zai faru.”

DABO FM ta tattaro gwamnan jihar Ribas ya kara da cewa; “Abin ya wuce tunani ace har yanzu gwamnan jihar Kano, Ganduje, yana da hallayar yin magana mara amana.”

“Naga takaradar da Gwamna Ganduje ya fitar akan cewa zai maka Gwamnan Ribas akan labarin karya na rushe Masallaci.

“Muna kara jaddawa, babu wani Masallaci da da Gwamna Wike ko gwamnatin jihar Ribas ta rushe.

An kirkiri labarin rushe Masallacin ne da wata manufa da Siyasa. Wani Alhaji Tobacco ne ya shirya labarin.

Manema labarai dayawa da kungiyoyi sun ziyarci gurin tare da tabbatar da babu abinda ya faru a wajen.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00