Fahad Danladi
Labarai

An fara darasin kallo na ‘Chemistry’ da harshen Hausa a tashar Youtube

An bunkasa rahotan ranar 07/01/2020.

A wani yunkuri na taimakawa daliban dake jin yaren Hausa yin karatun fannin kimiyya cikin sauki, dan Najeriya, Fahad Ibrahim Danladi (Fahad Kano), ya fara gabatar da darasin kimiyya a tashar Youtube.

Khalid Ibrahim, dalibi ne dake karatun Digirin-Digir-gir a jami’ar bincike ta UT Arlington dake birnin Texas na kasar Amurka.

DABO FM ta tattaro cewa Fahad Kano ya bayyana fara gabatar da darasin ‘Chemistry’ a wani faifan bidiyo da ya wallafa a sabuwar tasahar Youtube dinshi da ya ware domin yin darasin.

“Ina muku albishin cewar zan fara gabatar da kimiyya a harshen Hausa. Zan bada muhimmanci akan ‘Chemistry’ inda nafi kwarewa.”

“Zan yi kokari wajen bayanin darussan Chemistry na ‘yan makarantar Sakandire da Jami’a.”

Khalid Danladi, ya shaidawa DABO FM cewar zai rika fitar da karatun kowanne mako.

Za’a iya samun darussan a shafin Fahad Danladi a Youtube, Fahad Kano a Twitter da Instagram ko kuma a shafinshi na Facebook, Fahad Ibrahim Danladi.

Za’a iya kallon tallar da DABO FM ba ta da hurumi a ciki.
UA-131299779-2